ABNA24 : Rundunar sojojin ta ce bayanan dake cikin rahoton na HRW karairayi ne da ka iya tayar da husuma.
A ranar Litini data gabata ce kungiyar ta HWR, ta wallafa rahoton na ta, wanda a ciki ta soki sojojin gwamnatin Kamaru, da amfani da karfi wajen barnata dukiyoyi, da yin fyade, da hallaka jama’a ciki har da fararen hula, da kuma wawashe kayayyaki a yankin na arewa maso yammacin kasar.
To sai dai kuma cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Kamarun Cyrille Serge ya fitar, ya ce da ma dai HRW, ta sha daukar matakai daban daban, da nufin shafawa ayyukan tsaro, da jami’an tsaron kasar kashin kaji.
Jami’in ya kuma jaddada cewa, dukkanin zarge zargen dake cikin wancan rahoto ba su da tushe ko makama.
342/